Ahirrr dinku masu zafin kai a siyasar Najeriya musamman talakawa da zuri’arsu. Domin siyasar Najeriya ta zama babbar kasuwa ta bukata. Kowa hajarsa yake so ya siyar, wannan shine dalilin da yasa ake samun yawan canza jam’iyya.
Babu wasu makiyan juna a siyasar Najeriya da basu taba haduwa a jam’iyya daya ba. Shige-da-fice a siyasa ya dauko asali ne daga bukatar ‘yan siyasa na kujerar mulki. Ba za’a taba samun hadin kai ba a cikin tafiyar da aka tara mutane masu tsananin bukatar abu daya.
Wani masanin siyasa mai suna Thomas Hobbes yace “Duk sanda mutane biyu suka hada bukata ‘daya, to daga ranar sun zama makiyan juna. Kuma ita dama siyasa ta kunshi gwargwarmaya akan mulki, waye zai samu mulki, waye ba zai samu ba, menene hanyoyin da za’a hana Mr A ya samu mulki don Mr B ya samu.
Tsakanin jam’iyar APC da PDP har zabe yazo za’a dinga samun fita da shiga saboda duk sanda Mustapha ya nemi takara ba’a bashi ba dole zai yi tunanin komawa jam’iyyar da za’a bashi. Mafi yawancin ‘yan takarar shugabancin kasar Najeriya mutane ne wadanda suke da matsayi daya a siyasance.
Da yawa daga cikinsu tsofaffin gwamnoni ne da suka yi shekara takwas suna mulki don haka zai yi wahala a samu masalaha cikin sauki saboda kowa yana ji da kansa.

Sannan da yawa daga cikin jam’iyyun Najeriya sun ginu ne akan jari-hujja,suna taraiya ne da mutumin da yake da mamora shiyasa babu jam’iyar da bata da rikicin cikin gida. Dole zaka samu karan-tsaye da Karfa-Karfa a cikin ko wacce kungiya.
Allah ya kaimu zabe mai zuwa, insha Allah zamu ga alheri. Muna fata Allah ya zaba mana abunda yafi alheri. Amma siyasa ta fara daukar zafi, idanuwa sun fara rufewa, kowa ya ci burin tsayawa takara. Abokan hamayya da yawa sun samu hadin kai saboda su tinkari babban makiyi.
Amma abunda talaka bai sani ba shine, shin ko yana gabansu ko kawai suna yi ne don rufin asirin kansu kamar yadda aka saba a Najeriya. Sai dai abun mamaki, an samu wasu manyan ‘yan siyasa suna kuka saboda tausayin ‘yan Najeriya.
Saidai da yawa daga cikinsu sun taba yin mulki an gani,to bamu sani ba ko yanzu sun yi nadama ne suke shirin dawowa su gyara. An ci amanar talakan Najeriya, shekara kusan ashirin muna cikin wannan jam’huriyar amma har yanzu faqiran kasarmu sun haura miliyan tamanin.
Allah ya shiryar damu.
Daga Comrade M.K Soron dinki