CIN HANCI: An kwato naira miliyan 11 daga hannun wasu ‘yan sanda

0

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda mai kula da Karbar Koke-koken Jama’a, Abayomi Shogunle, ya bayyana yadda rundunar ‘yan sanda ta kwato naira miliyan 11 na kudaden cin hanci da ‘yan sanda ke karba a hannun jama’a a cikin shekaru biyu, a fadin kasar nan.

Shogunle ya yi wannan bayani a garin Osogbo a lkacin da ake gudanar da taron tsaftace jami’an ‘yan sanda da wayar musu da kai dangane da aikin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar 22 Ga Satumba.

Ya ce duk an mayar da wadannan kudade ga masu su, kuma an kori sama da ‘yan sanda 10 a kan laifin karbar cin hanci da kuma wasu laifukan da suka jibinci zubar da kima da darajar aikinndan sanda.

PREMIUM TIMES ta taba buga labarin yadda wasu ‘yan sanda ke karbar kudaden cin hanci ta hanyar tirsasawa, ciki kuwa har da wadanda ta nuna bidiyon yadda suke karbar kudaden daga hannun direbobi.

Daga nan sai ya hori jami’an da su guji karbar cin hanci domin duk wanda aka kama sai an hukunta shi.

Shogunle ya ce hukumar ‘yan sanda na bakin kokarin ta domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe sahihi kuma karbabbe a jihar Osun.

Ya ce ‘yan sanda za su kama duk wanda aka samu ya je kudade ya na rabawa a wurin zabe.

Share.

game da Author