Ku dawo gida daga kasashen da kuke, ana samun canji a Najeriya – Gwamnati

0

Gwamnatin Tarayya ta roki ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da su dawo gida su taimaka a gina Najeriya, tare da sha musu alwashin cewa al’amurran Najeriya na samun canjin ci gaba sosai.

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu ne ya bayar da tabbacin haka a wani taron ganawa da ya yi da ‘yan Najeriya mazauna Amurka.

Ministan ya je kasar Amurka ne domin ya gana da mazauna kasar ‘yan Najeriya a bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, domin karin samun kayan kimiyya, fasaha da kuma kayan fasahar.

Onu ya gode wa mazauna kasar musamman ganin yadda suka yi hulda da Najeriya har ta kusan dala biliyan 22 a kowace shekara.

Sai dai kuma duk da haka ya ce ana so su dawo gida.

“Duk mun ji korafe-korafen ku na baya da ku ka ce idan kun yi wani namijin kokari ba a kulawa da ku, to mun ji, amma wannan a da kenan ba a yanzu ba.”

Ya roke su da su maida hankali wajen dawowa gida tunda a yanzu dai komai ya fara tafiya daidai.

Sai dai kuma ya ce bai yiwuwa a ce su zauna a can har sai komai ya gyaru tukunna. Domin a cewar sa, ai da su ne za a hadu a gyara idan sun dawo gida.

Ya ce kowa ya yi tunanin irin muhimmin matsayin da ake so Najeriya ta kai a nan gaba. Don haka a daina kallon halin da ta ke a yanzu, a dawo gida a inganta arzikin kasar domin ta kara bunkasa sosai.

“Najeriya ta na da mashahuran mutane masu kaifin basira wadanda suka shahara har suka yi zarra a fannoni daban-daban a diniya.”

Da suke maida bayani, ‘yan Najeriya mazauna Amurka sun sha alwashin dawowa su taimaka a kara inganta Najeriya ta hanyoyi da dama.

Share.

game da Author