Hukumar Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bayyana cewa babu alamomin yin girgizar kasa a cikin Abuja da kewaye, kamar yadda aka Ji kasa ta yi jijjiga wasu yankuna, musamman a Mpape da kewayen unguwannin gefen ta.
An dai ji wannan jijjigar kasa ne a ranar Laraba da dare zuwa Alhamis da safe, a Abuja, ciki kuwa har da yankin mahadar Gishiri, mahadar NICON da sauran wurare.
Wannan jijjiga dai ta razana mazauna yankunan sosai.
Sai dai kuma Daraktan hukumar NEMA, Abass Idris, ya ce ba abin tayar da hankula ba ne.
A wata hira da ya yi da Kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN, a yau Juma’a, ya ce jijjigar kasar da aka ji a yankin Mpappe da wasu wuraren ciki har da Maitama, ba ya nufin akwai yiwuwar yin girgizar kasa a Abuja.
Ya ce wannan jijjiga ba ta rasa nasaba da wani irin karamin rugugin motsawar jijiyoyi ko igiyoyin da ke rike da kasa mai yiwuwa su tsinke yayin da motsawar ta wakana.
Wannan kuma inji shi, ba zai haifar da yiwuwar girgizar kasa ba.
“Lokacin da jami’an mu suka je wajen mazauna yankin Mpape, sun samu tabbacin cewa ba a wannan ne karon farko da hakan ta taba faruwa ba.
Sun ce an taba yin wannan jijigar kasa shekaru biyar da suka gabata.”
Sai dai kuma ya ce akwai bukatar a duk lokacin da hakan ta faru, to mazauna yankin su gaggauta ficewa su sake wuri, kafin jijjigar ta lafa.
Ya roki mazauna yankin idan sun ji irin haka, to su shige a karkashin tebura su boye idan su na cikin daki ne.
Ya ce kuma a kauce daga jikin tagogi ko kyauren dakuna a lokacin da kasar ke jijjiga.
Sannan kuma kada a tsaya kusa da gine-ginen gidaje, ko karkashin manyan bishiyoyi da turakun wutar lantarki.
Wani mazaunin Maitama mai suna Victor Okoye, ya ce da ya ji rugugin kara ya dauka dutsi ne ake fasawa, amma sai ya ji wannan rugugin ya fi karfin fasa dutse.
“Ai da na fito daga gida sai na fahimci dai kasa ce ke jijjiga. Nan fa hankali na ya ba ni cewa, ai shikenan, tashin kiyama ya zo.”
Wata mai suna Alice Adetola da ke Mpape kuwa, ta razana kwarai da gaske, ta ce haka su ma yaranta.
“Tashi na yi na rungume yara na, ina ta buga addu’a, domin na dauka ba za mu kai gobe ba.”
Discussion about this post