Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole da Gwamna jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu jigajigan jam’iyyar sun kai ziyarar zawarci gidan tsohon gwamnan Jihar Ibrahim Shekarau.
Bakin Shekarau sun kai wannan ziyara ne ranar Alhamis har gida.
Shekarau da manyan bakin sa sun gana tare da sauran ‘yan siyasa da ke tare da shi a lokacin ziyarar.
Ana sa ran ranar Asabar Ibrahim Shekarau da dubban magoya bayan sa za suyi gangamin ficewa daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Tare da Shekarau akwai ‘yan takarar gwamna shida, da mataimakin Shugaban Jamiyar PDP na jihar Kano da sakataren sa, shugabar mata, shugaban matasa da wasu da dama. Haka kuma akwai tsofaffin ‘yan majalisu, da kwamishinonin gwamnatin Shekarau da saura manyan magoya bayan sa.

Idan ba a manta ba tun bayan dawowar sanata Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar PDP aka fara samun rashin jituwa a tsakanin ‘yan siyasar biyu.
Abin da ya fara zama sanadi shine sauke shugabannin jam’iyyar na shiyyar jihar Kano da uwar jam’iyyar ta yi a Kano.
Hakan ya yi matukar yi wa bangaren Shekarau zafi inds suka koka cewa ana nuna fifiko ga Kwankwaso da ya dawo jam’iyyar.
Sannan kuma kakakin Shekarau ya bayyana wa tashar BBC Hausa cewa tsohon gwamnan ya fice daga PDP wadda daga baya Shekarau da kansa ya karyata haka a wancan lokacin.
Discussion about this post