ZABEN KATSINA: Babu abin da ya shiga tsakani na da dan-uwana – Ahmad Babba-Kaita

0

Sanatan da ya lashe zaben cike gurbi na shiyyar Katsina ta Arewa Ahmed Babba-Kaita ya karyata rade-radin da mutane ke yi cewa wai shi da wan sa Kabir Kaita basu ga miciji da juna tun bayan nasarar da ya yi a zaben cike gurbi da ka yi a jihar.

Idan ba a manta ba Hukumar Zabe ta Kasa ta gudanar da zaben cike gurbi na sanatan da zai wakilci gundumomin Kusada/Ingawa/Kankia a dalilin rasuwar sanata Bukar Mustapha.

Ahmad ya ce kusantar sa da dan-uwan sa ya wuce ta siyasa. Sunanan lafiya kalau babu abin da ya shiga tsakanin su.

” Ina so in shaida wa mutane da ke yayada karerayi cewa wai a dalilin nasarar da na samu a zaben da aka yi a jihar Katsina, mun samu sabani tsakani na da dan-uwana, Kabiru Baba-Kaita. Babu abin da ya shiga tsakanin mu.

Sannan kuma ya karyata cewa da aka yi wai siyan kuri’u yayi a zaben.

” Ban siya kuri’ar kowa ba. Ni da jam’iyyata muka dage muka nemi jama’a sannan muka tabbata an bi doka a zaben, a haka mu ka yi nasara.

Share.

game da Author