Gwamnati za ta hukunta duk dan kwangilar da ya yi aikin aliya a jihar – Bagudu

0

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu gargadi ‘yan kwangila da ke aiki a jihar da su tabbata sun yi aiki mai nagarta.

Bagudu ya bayyana cewa gwamnati ba za ta zuba ido ta bari wasu ‘yan kwangila na yin abin da suka ga dama a jihar cewa daga yanzu idan har dan kwangila yayi aikin aliya a jihar, zai kuka da kan sa.

Wannan gargadi da Bagudu yayi ya biyo bayan korafi ne da sarkin Zuru ya yi bisa ayyukan aliya da ‘yan kwangila ake yi a masarautar sa.

” Gwamnati ba zata ta zuba kudi a ayyuka a jihar ba sannan ‘yan kwangila su ki yin abin da aka yi alkawari da su. Dole mu zuba ido mu kuma tabbata an yi abin da ya kamata.

” Ku duba aikin Titi da ake yi a masarautar Zuru, ace wai yanzu-yanzu har hanyar da aka gina kwana-kwanan nan ya fara fashewa. Ba za mu amince da haka ba.

Share.

game da Author