Ana tauye mana hakki a jihar Jigawa – Mata masu zanga-zanga

0

Daruruwan mata a garin Dutse jihar Jigawa sun yi zanga-zanga don nuna fushin su ga gwamnatin jihar kan yadda aka mai da su saniyar ware a jihar.

Jagoran wannan zanga-zanga, Zainab Mohammed, ta bayyana cewa bayan saniyar ware da aka mai dasu musamman a harkar siyasa a jihar, mata a jihar na fama da hare-haren masu fyade, shaye-shayen kwayoyi da sauran su.

Ta ce dole ne gwamnati ta waiwaye su tun da wuri domin wahalar da suke sha a jihar ya ishe su hakanan.

Matan sun yi tattaki ne daga filin Aminu Kano zuwa gidan gwamnati. Kakakin majalisar dokokin jihar Idris Isah ya bayyan cewa lallai gwamnati za ta dauki mataki kan wadannan koke-koke nasu da suka taho da shi.

Wata ‘yar takarar gwamna a jihar Jigawa Habashiya Yelleman, ta ce ta lashi takobin kada gwamnan jihar a zaben 2019.

Share.

game da Author