TAMBAYA: Wane Abu ne Allah ya fi ki bawan sa ya aikata? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Wane Abu ne Allah ya fi ki bawan sa ya aikata? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Lallai Allah ta’ala yana kishi, kuma kishinsa ga bawansa she ne ya aikata abinda ya haramta. Kuma Allah yana son bawansa ya aikata abun alhairi kumai kankantarsa. Abubuwan da Allah ya fi ki daga wajen bawansa ya aikata sunada yawa. Babu karami ko babba a cikinsu, duk Allah yana kinsu. Wajibi ne bawa ya nisancesu don samun rahama.

ABUBUWAN DA ALLAH YA FI KI DAGA WAJEN BAWAN SA

1) Shirka da kafirci.

2) Barna da Almubazzaranci.

3) Zalunci, mugunta, ha’inci da keta.

4) Cin-dukiyar maraya da cin riba.

5) Girman kai, jiji da kai, dagawa da ganin kafi kowa.

6) Takama da alfahari.

7) Alfasha da munanan kalamai.

8) Bayyan tsiraici da hira yayin bayan gida.

9) Rashin aiki da ilimi.

10) Kisa da zubar da jini

11) Shigo da gargajiyanci (Jahiliyya) cikin addini.

12) Munafunci ko fuska biyu (Zulwajahaini).

13) Rokon wani bawa abinda Allah ne kawai ke badawa.

14) Tsananin husuma, gardama, jayayya da musu.

15) Yanke zumunta.

16) Umurni da mummunan aiki ko hani da kyakkyawa.

17) Kiran wani da sarkin sarakuna.

18) Mummunan raddi yayin da akace maka “Ji tsoron Allah”.

19) Kin tuba daga zunubai.

20) Karya.

21) Fatawa batare da ilimi ba.

22) Juya baya a filin Jihadi.

23) Zagin sahabbai ko kinsu.

24) Son doniya da jahilta lahira.

25) Ya wan tambaya da ba shi da amfani.

26) Jita-jita.

27) Sabawa iyaye.

Allah shi ne mafi sani

Share.

game da Author