Asibitin Bayelsa ya zamo zakaran-gwajin-dafi a kasar nan – Inji Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina fita zuwa kasashen waje domin wai ganin likita.

Obasanjo ya yi wannan kira ne a Jihar Bayelsa da ya ziyarci asibitin jihar domin yin wasu gwaje-gwaje.

Obasanjo ya bayyana cewa tabbas ya ji dadin irin kulan da ya samu da ya ziyarci asibitin.

” Gwaje –gwajen da na yi a wannan asibiti ya gamsar da ni matuka domin aiyukkansu daidai yake da wanda muke samu a kasashen waje. Saboda haka babu wani amfani mutum ya kashe makudan kudi wajen fita waje neman magani idan muna da irin wadannan asibitoci a kasar nan.”

A karshe Obasanjo ya jinjina wa gwamnan Seriake Dickson kan wannan namijin kokari da yayi wajen gina irin wannan katafaren asibiti a jihar ya yi sannan ya hori mutanen da nauyin kula da wurin ya rataya a hannun su da su ci gaba da aikin da suke yi a yanzu haka koda wannan gwamnatin ta sauka.

Obasanjo Check up

Obasanjo Check up

Share.

game da Author