Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga mata a Najeriya da su daina haihuwa a gida sannan a daina bari wanzaman da basu kware ba suna yi wa wa jarirai kachiya da cire belubelu.
Ya ce hakan na cikin hanyoyin da ke sa a kamu da a cutar dake kama hanta wato ‘Hepatitis’.
Adewole yace cutar Hepatitis cuta ce dake kama hantar mutum sannan akwai ta kamar haka Hepatitis A,B,C,D da E kuma ba a iya gane cutar a jikin mutum ya dade a jikin sa.
” Bincike ya nuna cewa duk shekara cutar na yin ajalin mutane miliyan 1.3.
” A Najeriya kuwa mutanen dake dauke da wannan cuta sun kai miliyan 20 sannan da dama cikin su basu san suna dauke da ita ba.
Adewole ya ce za a iya kamuwa da wannan cuta ta hanyar yawan shan giya, yawan shan magunguna, yin amfani da kayan aikin da basu da tsafta wurin karban haihuwa, kaciya, cire da sauran su.
Ya ce burin gwamanin kasar nan shine ta ga cewa ta kawar da wannan cutar kafin nan da shekaran 2030.
Discussion about this post