Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole, ya bayyana cewa ‘yan siyasa a kasar nan na neman su nuna wa duniya cewa matsalar tsaro a kasar nan wani rikici ne na kabilanci, ta hanyar dora wa wata kabila laifi domin biyan wata bukata ta su ta siyasa.
Sai ya yi kira ga ‘yan Najeriya kada su bari wasu su yi amfani da wannan karairayin su yaudare su.
Oshimhole ya bayyana haka a garin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi yayin da ya ke bayanin murnar karbar sabbin shigar jam’iyyar APC da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP a jihar.
Ya ce akwai kokari da wasu ‘yan siyasa ke yi su nuna cewa gwamnatin Buhari na da masaniyar cewa kashe-kashen da ake yi a wasu jihohin kasar nan duk ayyukan Boko Haram.
“Ina jan hankalin ku da cewa an shiga kakar da ake ta yada ji-ta-ji-ta wadanda ba gaskiya ba ce. Ana daukar mutane sojojin haya su na birkita karya su ce ita ce gaskiya. Su na so mu yarda cewa kowace matsala a danganta ta da kabilanci da addini.
Ya kara da cewa Shugaba Muhammadu Buhari da sauran manyan jami’an sun a aiki ba dare ba rana domin ganin kawo karshe.
Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu, ya tunatar da yankin Kudu Maso Gabas cewa a zaben 2015 sai da ya yi musu gargadin cewa kada fa su zuba kwayayen su a cikin Kwando daya su zabi PDP kadai.
Daga nan sai ya yi kira kada su sake yin wannan kuskuren a zaben 2019.
“Duk da a wannan yanki kuri’u kashi 10 bisa 100 kadai aka ba Buhari a zaben 2015, ku dubi abin alherin da ya yi wa wannan yanki. To ina ga idan ku ka zuba masa kuri’u kashi 75 bisa 100 a 2019, wane irin gagarimin aiki ne ba zai yi mana ba? Inji Minista Onu.