Matalauta da fakiran Najeriya sun fi na kowace kasa yawa a duniya –Theresa May

0

Firayi Ministar Birtaniya, Theresa May, ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 87 a Najeriya, na fama da talaucin da ba su iya samun akalla dalar Amurka biyu a rana, kwatankwacin naira 700 a kowace rana.

Ta ce hakan ya jefa wadannan fakirai na Najeriya a matsayin wadanda suka fi al’ummar kowace kasa ta duniya fama da talauci da fakiranci.

Ta yi wannan bayani jiya Talata, kwanaki daya kafin ziyarar da ta shirya kawowa a Najeriya, ranar Laraba a Abuja.

Jawabin na ta wanda aka buga a wata yanar intanet ta Gwamnatin Birtaniya, ta ce akasarin ‘yan kasar Afrika duk matalauta ne fafur.

“Misali, duk da mutane da yawa na more rarrafen da tattalin arzikin Najeriya, amma idan aka yi la’akari da cewa kusan jama’a milyan 87 a Najeriya basu iya samun dala 1.90 a rana, hakan ya sa kasar ta fi sauran kasashen duniya masu fama da wayan matalauta da fakirai.” Inji May.

Wannan kalami na ta zai iya zama makamin da ‘yan adawa za su iya rikewa domin yin zazzafar suka ga gwamnatin Buhari da kuma gurguwar turbar da suke ganin ya na bi da tsarin tattalin arzki.

“A Afrika yawancin mutanen da ke fama da talauci suke. Bunkasar masu dukiya ya kara haifar da wawakeken rata da tazara a Najariya da Afrika.”

“Bugu da kari kuma ga Boko Haram da al-Shabab na ci gaba da kashe mutane ba-ji-ba-gani.

“Tekun da ke kewaye da gefen Afrika, wanda ya nunka tsandaurin kasa kusan sau uku wajen fadi, shi ma ya na cikin barazana, domin ana ci gaba da gurbata ruwan sa da dagwalon kazanta da kuma bolar da tulin jujin tarkacen robobin da aka ci aka shanye abin da ke ciki aka jefar.” Inji ta.

Share.

game da Author