KWALARA: Kananan hukumomi 10 a jihar Barno sun kamu

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Barno Haruna Mshelia ya bayyana cewa mutane a kananan hukumomi 10 dake jihar sun kamu da cutar kwalara.

Ya ce akalla mutane 1068 sun kamu da cutar a jihar sannan daga ciki 25 na samun kula a asibitocin dake Benishek,Dala da Elmiskin.

Mshelia ya koka kan yadda mutane ke yin bahaya a ko ina sannan da rashin tsaftace muhalli musamman a sansanonin ‘yan gudun hijra.

” Ya zama mana dole mu tsaftace muhallin mu, jikkunan mu da abincin da za mu ci don guje wa kamuwa da wannan cuta.

” Duk da cewa ba a rasa rai ko daya ba gwamnati za ta zage damtse wajen ganin ana wayar wa mutane kai gane da cutar akai-akai game da mahimmancin tsaftace muhalli.

A karshe ya ce ma’aikatan kiwon lafiya su za su gudanar da bincike don gano musabbabin bullowar cutar sannan bayan haka za su aikawa hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) sakamakon binciken su.

Share.

game da Author