Jami’in shirin ciyar da daliban makaranta na gwamnatin tarayya (NHGSFP) Aliyu Abdulkadir ya bayyana cewa gwamnati ta horas da mutane 2746 masu girka wa daliban makarantun firamare abinci.
Ya fadi haka ne a taron kaddamar da wannan shiri da aka yi a Lafia ranar Talata.
Abdulkadir ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ta tsara wannan shiri domin inganta ilimin da yara ke samu a makarantun gwamnati dake kasar.
Ya kuma ce shirin za ta taimaka don samar wa mutane (maza da mata) aikin yi sannan hakan zai bunkasa aiyukkan noma a jihar.
” Wannan shirin hadin guiwa ne na gwamnatocin jihohi, na tarayya da kananan hukumomi, sannan shirin za ta fara ciyar da daliban makarantun firamare daga aji daya zuwa uku ne.
Abdulkadir ya ce gwamnati ta horas da wasu mutane daban da za su rika kula da tsafta da ingancin abincin da za a rika girka wa.
Bayan haka mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da yake nashi tsokacin a kai ya bayyana cewa wannan shiri na ciyar da yara sama da miliyan 7.6 abinci a jihohi 22 na kasar nan.
Discussion about this post