Ko na fadi zaben fidda gwani ba zan fice daga PDP ba –Inji Sule Lamido

0

Tsohon gwamnan jihar Jigawa wanda dan takarar shugabancin Najeriya ne a karkashin jam’iyyar PDP Sule Lamido ya bayyana cewa ba zai fice daga jam’iyyar ba koda ya fadi a zaben fidda gwani.

Ya bayyana haka ne a ganawa da ya yi da manema labarai a garin Jos, bayan ganawa da ya yi da Jeremiah Usaini.

Idan ba a manta ba a kwankin bayan Lamido ya ziyarci jihar Filato inda ya sanar ya ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar muradin sa na yin takarar shugabancin kasa Najeriya.

Ya ce duk wadanda suka fito takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP na da kwarewa kuma yana da yakinin cewa dukkan su na yi don kasa ne ba don san kan su ba.

” Wannan shine babban dalilin da ya sa ko da na fadi zaben fidda dan takara ba zan fice daga jam’iyyar ba, saboda akidar mu daya ne dukkan mu.

Bayan haka Lamido ya karyata rade-radin da ake ta yadawa cewa wai ya fito takarar shugabancin Najeriya ne da daurin gindin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

” Ina tabbatar muku da cewa da zaran na zama shugaban kasa a Najeriya zan tabbatar da tsaro a ko-ina a kasar nan sannan zan bunkasa tattalin arzikin kasa.

Share.

game da Author