Ambaliyar ruwa ya ci kananan hukumomi takwas a jihar Kano

0

Shugaban hukumar bada gajin gaggawa na jihar Kano (SERERA) Ali Bashir ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ya ci kananan hukumomi takwas a jihar.

Ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a garin Kano.

Ya ce hukumar ta aika da ma’aikatan ta domin duba iya barnar da ambaliyar ya yi a wadannan kananan hukumomin.

” Kananan hukumomin da ambaliyar ya shafa sun hada da Rimin Gado, Tofa, Dawakin Tofa, Gwarzo, Danbatta, Kabo, Gezawa da Gabasawa.

Bashir ya kara da cewa ba zai iya fadin adadin yawan mutanen da ambaliyar ruwar ta shafa ba da yawan dukiyoyin da aka rasa domin har yanzu ma’aikatan su basu kammala aiyukkan da suke yi a garuruwan ba.

Ya ce da zaran sun kammala za su gabatar wa gwamnatin jihar Kano da sakamakon binciken da suka yi.

A karshe bayanai sun nuna cewa mutane uku sun mutu sannan gidaje da dama sun rushe a karamar hukumar Kiru.

Share.

game da Author