Gwamnatin Jihar Benuwai ta bayyana cewa Hukumar EFCC ta kulle mata asusun kudin ta na banki, inda albashi da kudaden fanshon ma’aikatan jihar ke ciki.
Kakakin Gwamna Samuel Ortom mai suna Terver Akase ne ya bayyana haka ga PREMIUM TIMES a yau Laraba.
“Wannan fa duk wani sabon babin bi-ta-da-kulli ne ake yi wa Gwamna Samuel Ortom. Dama kuma abin da EFCC din ta yi wa gwamnatin ya kawo tarnaki da cikas wajen tafiyar da gwamnatin jihar Benuwai. Sannan abin ya shafi biyan albashi da sauran kudaden fansho.”
Wannan bayani na sa, ya zo kwana daya bayan da jaridar Vanguard ta buga labarin cewa EFCC ta kulle asusun ajiyar gwamnatin jihar Benuwai guda uku da ke GTBank, First Bank da Fidelity Bank.
Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa EFCC na binciken gwamna Ortom da zargin cewa watakila kamar ya karkatar da naira biliyan 22.
Ortom ya ce abin duk karya ce da rashin kunya kawai, ana yi ne don a kawar da shi daga gwamnan jihar Benuwai, saboda haushin ya fice daga APC ya koma PDP.
Akase ya gargadi EFCC da cewa kada ta bari mutuncin ta ya zube ta hanyar bada kofa ana amfani da ita domin biyan bukatar siyasar wadanda ke kan gwamnatin tarayya.
“Tambayar da mu ke yi ita ce me ya sa ba a tashi binciken ba sai da ya fice daga APC?
“Don me ba a bincike shi ba a lokacin da ya na APC”.
An toshe asusun kwana daya bayan da Ortom ya yi wa gwamnatin tarayya wankin babban bargo, kuma ya fice daga APC.
Discussion about this post