Hauwa ta roki kotu da ta tilasta wa mijin ta ya rika biyan ta kudin shayar da dan su

0

Wata mata mai suna Hauwa, mazauniyar garin Kaduna ta roki Kotu da ta tilasta wa mijin ta mai suna Maibulala Rabiu da ya rika biyan ta kudin shayar da dan su, Sulaiman.

Hauwa ta shigar da kara a kotun Shari’a dake Kaduna ne in da ta ce tun bayan sakin ta da Maibulala yayi ranar 31 da watan Yuli bai aiko mata da kudin da zata rika ciyar da dan su ba dahar yanzu yana shan nono ne.

Sai dai kuma mijin Hauwa, wato Maibulala, ya bayyana wa kotu cewa a gaskiya baya aiki ne kuma bashi da kudin da zai iya bata, a dalilin haka ya roki kotu ta yardan masa ya rika aika wa Hauwa naira 3000 duk wata domin shayar da dan nasu.

Alkalin Kotun ya amince da wannan roko na Maibulala, sannan ya bukace shi da ya rubuta wa matar sa Hauwa takardar saki maimakon da baki da ya furta a wancan lokaci.

Share.

game da Author