Na shiga APC domin na taimaka a kawar da yunwa a Najeriya – Akpabio

0

Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, kuma Sanata, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar APC ne daga PDP, domin ya taimaka a kawar da yunwa da karfa-karfa a Najeriya.

Da ya ke bayani a wurin gangamin yi masa wankan shiga jam’iyyar APC, y ace ya koma jam’iyya mai mulki domin ya kai gagrimin ayyukan ci gaba a yankin Kudu-maso-Kudu.

An yi wannan gangami a garin Ikot Ekpene, cikin filin wasan garin, wanda ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC.

Ya shaida wa dandazon mutanen da suka halarci yi masa wankan tsarkin komawa APC cewa Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma mai kishin Najeriya.

Ya kara da cewa Najeriya na fama da yake-yake ta kowane bangaren kasar nan. Don haka akwai bukatar ire-iren su su hada hannu domin a samu tabbatacin zaman lafiya a kasar nan.

Idan ba a manta ba, ranar 4 Ga Satumba, 2015, jami’an DSS sun yi wa gidan Akpabio dirar-mikiya, inda a cikin wani daki suka bayyana cewa an samu wasu muggan makamai da tulin albarusai da kuma tsibin milyoyin daloli.

Akpabio ya garzaya Uyo daga Abuja domin zuwa gidan na sa, sai dai kuma direban san a cikin fanfalar gudu da nufin ya kai shi fillin jirgi, sai motar su ta yi hadari a daidai mahadar titin otal din Bolingo da ke Abuja.

Wannan hadari ya kai sai da aka dauki Akpabio zuwa asibitin Turai.

Ranar 4 Ga Agusta kuma ya koma jam’iyyar APC.

Share.

game da Author