Kwankwaso zai yi gangamin kaddamar da takarar shugaban kasa a Abuja

0

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zai gangamin kaddamar da takarar shugaban kasa a Abuja ranar Laraba.

Binta Sipikin ta bayyana haka a takarda da ta saka wa hannu a madadin Kwankwaso.

Sipikin ta ce babban dalilin da ya sa za a yi kaddamarwar a gari Abuja shine don nan ne mahada.

” Abuja ne babban birnin tarayyar Najeriya sannan mahada. Tunda takarar na kasa ne kowa ya taso Abuja zai fi masa saukin zuwa.

” Taron ba ta Kano ba ce, taro ne da ya shafi kasa baki daya, shine yasa muka zabi muyi a Abuja.” Inji Sipikin.

Za ayi taron ne ranar Laraba, a filin Eagle Square dake Abuja.

Share.

game da Author