Hajji 2018: Jirgin Farko ya sauka dauke da Alhazan Abuja

0

Tawagar Alhazan farko da aka yi jigila daga kasar Saudiyya sun sauka a filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 5:30 na safiyar Litinin.

Jirgin Flynas Flight XY7744, dauke da Alhazai 225 daga Abuja ne ya dawo da su.

Wani jirgin ya riga ya taso daga kasar Saudiyya dauke da Alhazan Sokoto 249 da kuma jirgin MaX dauke da Alhazan Kogi 446 duk suna kan hanyar su na dawo wa kasa Najeriya.

Ana sa ran jirgin dake dauke da Alhazan Sokoto zai sauka a filin jirgin sama na Sultan Abubakar, da misalin karfe dayan rana.

Share.

game da Author