Jami’an EFCC sun kama wani Babban Manajan Daraktan bankin Zenith Bank, Peter Amangbo, bankin da ya fi kowane bankin kasuwanci karfin arziki a duniya.
An damke shi ne a yau Lahadi, bayan da aka fara binciken wata bahallatsa da harkalla shige da ficen kudade na jihar Rivers, jihar da ta fi kowace jiha arzikin man fetur a Najeriya.
EFCC na zargin akalla an karkatar da naira biliyan 117, amma kuma bankin na Zenith sun kasa yin bayanin kudaden kamar yadda doka ta tanadar.
Wata majiya daga EFCC ta ce an kama Amangbo ne domin ya yi bayanin dalilin da ya sa bankin Zenith ya kasa daukar bayanan cire wadannan makudan kudade, wadanda aka rika jida a cikin shekaru uku.
Tun da farko dai an gayyaci Amangbo zuwa EFCC domin a yi masa tambayoyi, amma sai aka bada belin san a kai tsaye, aka ce ya koma a washegari ranar 24 Ga Agusta domin a ci gaba da tambayoyi.
Sai dai kuma majiyar mu ta ce yayin da ya kai kan sa ofishin EFCC a ranar Juma’a sai aka tsare shi aka hana shi tafiya gida.
An kuma tabbatar da cewa a yau Lahadi da misalin karfe 4 na yamma, an yi ta sheka masa ruwan tambayoyi.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa baya ga shi, ana kuma neman wasu jami’an gwamnati su hudu wadanda tuni suka cika wandon su da iska.
An ce Daraktan Kudade da Kididdiga, Fubara Similari na Gidan Gwamnatin Jihar Rivers, ya ari takalmin kare ya falfala a guje.
Shi ma mai biyan kudi a Gidan Gwamnatin Jihar ya dafe keya ya arce.
Jami’an yada labarai na bankin Zenith da PREMIUM TIMES ta tuntuba, sun ki cewa komai. Akin Olaniyan da kuma Victor Adoji ba su amsa kiran da wakilin PREMIUM TIMES ya yi musu ba.
Sai dai kuma gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya fassara kamen da cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai. Ya ce zai ci gaba da kare jami’an gwamnatin sa daga zuwa amsa tambayoyi a ofishin EFCC.
“Ba wani jami’in gwamnatin jihar Rivers da zai je ofishin EFCC domin a yi masa tambayoyi.” Haka kakakin yada labaran sa Simeon Nwakaudu ya bayyana a cikin wata takardar manema labarai a yau Lahadi.
Wike ya ce Kotun Daukaka Kara a cikin 2007 ta haramta EFCC ta rika leka asusun ajiyar jihar Rivers, ya ce kuma har yau dokar na nan, ba a daukaka ta ba.
Wannan kakuduba ta kunno kai ne makonni biyu bayan da EFCC ta kulle asusun Jihohin Benuwai da Akwa Ibom, jihohin da duk na ‘yan adawa ne.
Wike ya ce babu ruwan EFCC da asusun jihar Rivers, hakki ne na majalisar jihar ba na EFCC ba.