• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

    Askarawan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 42, sun kama 20 sannan sun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su – DHQ

    Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru

    Crisis in Jos

    BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW

    GUDUN YIN BIYU-BABU: Gwamnan Bauchi ya sayi fam ɗin sake yin takarar gwamna, daidai lokacin da ya fito takarar shugaban ƙasa a PDP

    Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa – Bala Mohammed

    Kano State Assembly

    Dan majalisar dokoki na jihar Kano ya doka ‘Ribas’ bayan ya tsunduma lambun jam’iyyar NNPP, ya ya rungumi tsintsiyar sa ya dawo APC

    Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

    Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

    Nigerian Pilgrims

    HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

Cikar Ni’imar Allah Ga Masu Niyyar Yin Layyah – Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
August 11, 2018
in Ra'ayi
0
Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Bismillahir Rahmanir Rahim

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai. Muna gode masa, muna neman taimakonsa. Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da miyagun ayyukan mu. Lallai wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma wanda ya batar babu mai shiriya a gare shi. Kuma ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad Bawan sa ne kuma Manzon sa ne.

Ya ku bayin Allah masu girma! Lallai babu shakka, idan watan zul-Hijjah ya kama, shigowar sa ko ganin sa ya tabbata, shugabanni da Allah ya dora wa nauyin yin sanarwa suka yi sanarwa, kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to an hana shi ya rage gashi ko ya aske gashi a jikin sa. Haka kuma an hana shi ya rage farce/kumba/akaifa, ko ya rage wani abu daga cikin fatar jikin sa. Amma ba’a hana mata masu niyyar yin ibadar layyah, yin Kitso ko lalle/kunshi ko sanya turare ba, kamar yadda naji wasu suna fada.

Kuma ya kamata mu sani, wannan hukuncin ya shafi mai niyyar yin layyar ne kadai, ban da matansa da sauran iyalin gidan sa. Haka nan hukuncin bai shafi wanda aka sanya shi matsayin mai wakiltar layyar wani ba, koda shine zai yanka. Wannan hukuncin ya shafi mai niyyar layyah ne kadai, ya hada namiji da mace duk daya ne, in ban da maganar kitso da lalle.

Hujjah akan wannan shine ingantaccen Hadisin uwar Muminai Ummu Salmah (RA) tace:

“Lallai Manzon Allah (SAW) yace: Idan aka ga watan Zul-Hijjah kuma dayan ku yayi niyyar yin Layyah, to ya kame daga aske gashin sa da farcen sa.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

A wata ruwayar yana cewa: “Kada ya rage wani abu daga gashin sa ko fatar sa.”

* Fahimta Da Maganganun Malamai Game Da Wannan Hadisi

Hakika malamai sun tattauna, kuma sun karawa juna sani game da wannan Hadisin. Ibn Musayyib yana cewa: Da Rabi’atu Ibn Abdurrahman da Imam Ahmad da Imam Is-haq da Dawud da wani bangare na Mabiya shafi’iyyah sun tafi akan cewa:

“Haramun ne ga mai niyyar yin layyah idan watan Zul-Hijjah ya kama ya rage gashi ko farce ko wani abu a fatar sa, har sai ya yanka dabbar layyar sa, saboda Hadisin da yazo a zahiri yana hukunta haka…” [Duba Sahihu Fiqhus-Sunnah wa Adillatuhu, mujalladi na 2, shafi na 375]

Sannan Imamu Malik da Imamu Shafi’i, mabiya shafi’iyyah, sun tafi akan cewa:

“Yin hakan makaruhine, wato ka yanke farce ko ka aske gashi. Hani ne na karhanci da kyamata, ba haramun bane, saboda Hadisin Nana Aisha (RA)…” [Bukhari da Muslim]

Sannan Majalisar Koli ta kwamitin Malaman Kasar Saudiyyah wato Al-Lajnatid Da’imah, sun bada fatawa cewa:

“An shar’anta wa mai niyyar yin layyah cewa, idan an ga watan Zul-Hijjah kada ya rage wani abu daga jikin fatar sa ko gashin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa. Saboda Hadisin da Malaman Hadisi guda shida suka ruwaito in banda Imamul Bukhari, daga Ummu Salmah (RA), tana cewa lallai Manzon Allah (SAW) yace: “Idan anga jinjirin watan Zul-Hijjah kuma dayan ku yana da niyyar yin Layyah, to kada ya rage wani abu daga gashin sa ko farcen sa.”

A cikin lafazin da Imam Abi Dawud da Muslim da Nasa’i suka ruwaito yana cewa:

“Wanda yake da abin layyar sa idan watan Zul-Hijjah ya kama kada ya rage wani abu daga gashin jikin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa.” [Duba Fatawa Al-Lajnatid Da’imah, mujalladi na 11, shafi na 397-398]

Sannan Imam Muhammad Ibn Hazm (rahimahullah) yana cewa:

“Wanda yake so yin Layyah idan aka ga sabon watan Zul-Hijjah to wajibi ne a kan sa kada ya rage wani abu na gashin jikin sa ko farcen sa, har sai ya yanka abin yankan sa. Amma wanda baya da niyyar yin layyah wannan hukunci bai hau kansa ba.” [Duba Al-Muhallah na Ibn Hazm]

Sannan Imam Ibn Qudamah (rahimahullah) yana cewa:

“Idan tsayuwar watan Zul-Hijjah ya tabbata, to mai niyyar yin Layyah zai kame daga yanke farce da aske gemu idan kuma yayi hakan to sai ya nemi gafarar Allah, babu fansa a kan sa a bisa haduwar Malamai, kuma ya aikata hakan da mantuwa ne ko da gangan.” [Duba littafin Al-Mugni, mujalladi na 9, shafi na 346]

Sannan Imamu Shawkani (rahimahullah) yana cewa:

“Hikimar da ke cikin hani akan rage gashi ko farce ga mai niyyar yin layyah shine, domin ya sami cikakkiyar ladar sa ta layyah, na samun ‘yantawa gaba daya daga wuta zuwa Aljannah, domin kuma yayi koyi da mai yin aikin Hajji cikin Ihrami, an hana shi wadannan abubuwa a lokacin aikin Hajji har sai ya gama jifar farko. To kai ma a nan gida sai aka sanya kayi hakan don samun ladar ibadah irin ta shi…” [Duba littafin Nailul Autar na Imamu Shawkani, Mujalladi na 5, shafi na 133]

* Nasihata Ga Malaman Da Suke Karyata wannan Sunnah Ta Hana Yanke Farce Da Aske Gashi Ga Mai Niyyar Yin Layyah!

Ya ku ‘yan uwa! Lallai ina kira da nasiha ga wadannan Malamai da suji tsoron Allah, su daina izgilanci da Hadisan Annabi (SAW) da sunan bin Mazhaba ko bin wani Malami. Su daina yada irin wannan sabani, domin kaucewa rudani da haifar da rarrabuwa a cikin al’ummah. Suji tsoron Allah, su tabbatar da abinda ya tabbata da ingantattun hujjoji, su daina kore duk wani abu da nassi ya tabbatar da shi, kawai don son zuciyar su da kuma neman a sansu, ko don girman kai, da kin karbar gaskiya.

Wannan mas’alah ba sabuwar mas’alah bace. Malamai magabata nagartattu, masu ikhlasi da tsoron Allah sun yi bayanin ta. Don haka, a yau wani yazo da rana tsaka ya nemi rusa abinda ya tabbata kuma ya inganta a Hadisin Annabi (SAW) kawai don son zuciyar sa, ko don dakusasshen ra’ayin sa, sam wannan ba zai karbu ba, kuma al’ummah ba zasu taba yarda da shi ba. Allah ya nuna muna gaskiya ya bamu ikon bin ta, ya nuna muna karya ya bamu ikon guje mata, amin.

Wassalamu Alaikum,

Allah yasa mu dace, kuma Allah ne mafi sani.

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Najeriya. Za ku iya tuntubar Imam a: gusaumurtada@gmail.com ko +2348038289761.

Tags: AbujaGusauIslamLayyaMusulunciNajeriyaOkenePREMIUM TIMESSallah
Previous Post

Gwamnati ta ciyo bashin dala miliyan 150 don kawar da cutar shan inna a Najeriya -Kemi

Next Post

Osinbajo zai kai ziyara Zamfara ranar Talata

Next Post
Yemi-Osinbajo

Osinbajo zai kai ziyara Zamfara ranar Talata

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ƴan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane uku a Adamawa
  • Dalilin da ya sa za mu ƙirƙiro gundumomi 268 a jihar Filato – Lalong
  • TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo
  • TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba
  • Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wata moto cike makil da kayan haɗa nakiya, harsasai da bindigogi

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.