Ministan harkokin Kudi Kemi Adeosun ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ciyo bashin dalla miliyan 150 daga bankin duniya domin kawar da cutar shan inna.
Kemi ta sanar da haka ne bayan kammala taron kwamitin zartaswa da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shugabanta a makon da ya gabata.
A bayanan da ta yi Kemi ta ce gwamnati za ta yi amfani da wannan kudade ne wajen siyo maganin rigakafin da za a yi amfani da shi wa yara.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamnatin Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya shirinta na ganin cewa ta kawar da cutar shan inna a kasar ta hanyar wadatar da jihohin kasar nan kudade domin kawo karshen cutar.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da hakan a taron da aka yi don samar da mafita kan hakan.
Osinbajo ya ce cutar shan inna ta sake bullowa ne bayan kasa Najeriya ta yi shekaru uku ba’a sami sanarwan sake bullowar ta ba.
Ya ce hakan ya faru ne saboda aiyukkan kungiyar Boko Haram da ya hana ma’aikatan rigakafin cutar shiga wasu garuruwa a yankin.
Ya kuma ce gwamnatin Najeriya za ta wadata jihohin da duk kudaden da suke bukata domin kawar da cutar gaba daya a kasa Najeriya.
Discussion about this post