Osinbajo zai kai ziyara Zamfara ranar Talata

0

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, zai kai ziyara jihar Zamfara a ranar Juma’a.

Osinbajo zai je ne domin duba wasu ayyuka da za a kaddamar a Jihar, a Kananan Hukumomin Talata-Mafara da Bakura.

Ziyarar inji Liman ta na daga cikin shirye-shiryen da ake yi domin bikin cikar Gwamna Abdul’aziz Yari shekaru bakwai a kan mulki.

Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Lawal Liman ne ya bayyana haka, tare da cewa wasu ayyukan da Osinbajo zai kaddamar har da Kwalejin ‘Yanmata ta Talata Mafara, Titin Bypass na Talata Mafara da kuma Makarantar Kwararru ta Tinau Special Primary School a Mafara.

Akwai aikin ruwa na garin Gamji da kuma kwaskwarimar da aka yi wa Babban Asibitin Bakura.

Y ace akalla akwai ayyuka sama da 100 da ake sa ran kammalawa daga nan zuwa watan Nuwamba.

Ana kuma sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar a cikin watan Satumba, 2018.

Share.

game da Author