Abin da Gwamnonin APC suka tattauna da Buhari – Okorocha

0

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, ya bayyana cewa hankalin Buhari bai tashi ba dangane da yadda hasalallu ke yi wa jam’iyyar APC fitar-farin-dango ba.

Okorocha ya bayyana haka a jiya Laraba da dare ga manema labarai na Gidan Gwamnatin Tarayya, jim kadan bayan da gwamnatin na jam’iyyar APC suka fito daga wata ganawar gaggawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

An yi taron ne a cikin Babban Dakin Taron da ke ofishin Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari.

Okorocha ya ce sun gana sannan sun tattauna da Buhari ne domin su shaida masa cewa har yanzu APC ta na da gwamnoni har 22, kuma jam’iyyar zaune ta ke daram da gindin ta.

“Mun gana ne domin mu fada masa cewa mu zaratan sa mu na nan a cikin shiri, kuma shi ma ya dau azama da nuna rashin kasala.

“Kai mu fa Buhari har ce mana ya yi a yanzu haka idan ya kwanta barci sai ya saita agogo mai kararrawa domin ya tsahe shi daga barci. Idan ba haka ba kuwa sai ya yi ranar barci.” Inji Okorocha, yayin da yace kwamacalar ficewa daga APC ba ta hana shi barci.

Okorocha ya kara cewa a yanzu ne ma APC ta fi karfi fiye da can baya.

“Mu na da jihohi 22, sanatoci 53. Har yanzu dai mu ne da rinjaye kenan, kuma mu na fatan za mu samu karin wasu su shigo a cikin jam’iyyar mu.

Ya ce tuni dama su na da masaniyar cewa wadanda ke ficewa daga jam’iyyar, ko badade, ko bajima ficewa za su yi.

Share.

game da Author