Ban fice daga APC ba – Minista Aisha Alhassan

0

Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan, ta bayyana cewa har yau ta na nan a kan mukamin ta na minista a cikin Gwamnatin Tarayya.

Ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke wata tattaunawa da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ta bayyana cewa har yau ba ta sauka daga cikin gwamnati ba.

“Sabanin yadda wasu ke takad-da-kanzon-kurege a yanar gizo, to ban sauka daga cikin gwamnati ba, amma abin da kawai na yi shi ne na nemi izni wajen Shugaba Muhammadu Buhari domin na je gida ko na ce jiha ta na fara tuntubar jama’a ta.

“Wannan kuwa ai shirye-shirye ne kawai domin neman a tsaida ni takara daga cikin jam’iyyar mu mai albarka, APC, domin na tsaya mata takarar gwamnan jihar Taraba a zaben 2019. Kuma Buhari din ya amince, har kuma ya yi min fatan alheri.

“Don haka wasikar da aka rika watsawa a yanar gizo, ai ba ta na nufin na sauka daga mukami na na minista ba ne.” Inji Mama Taraba.

Ta yi kira ga daukacin masoyan ta na jihar Taraba, musamman ma mata da su yi watsi da surutan da ake yadawa wai ta sauka daga mukamin ta.

Share.

game da Author