Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya ware Naira biliyan 1.2 daga cikin biliyan uku da ya yi alkawarin samarwa domin gina asibitoci a mazabu 105 dake fadin jihar.
Dickson ya fadi haka ne a wani taro da akayi domin inganta lafiyar mutanen jihar musamman mata da yara kanana ranar Talatar da ta gabata.
Dickson ya kuma kara da cewa zai ware Naira miliyan 100 domin biyan kowace mace mai ciki a jihar alawus din Naira 3000 duk wata har sai ta haihu.
” Sanin kowa ne cewa mutuwan mata masu ciki da yara kanana na neman zama ruwan dare a wannan jihar wanda haka ya zama mana dole mu nemi mafita daga wannan matsalar.
” Bayan karin asibitocin da za mu gina kowace mace mai ciki zata rika karbar alawus din Naira 3000 duk wata har sai ta haihu.
Gwamna Seriake ya bayyana cewa matan da suka yi rijistan yin awon su a asibitocin gwamnati ne kawai za su na rika samun wannan kudade.
A karshe ya ce gwamnatin sa za ta hada hannu da sarakunan gargajiya da masu fada a ji a jihar domin ganin an sami raguwar yawan mace-macen mata da yara a jihar.