Taron Majalisar Zartaswar Tattalin Arzikin Kasa a yau Alhamis ya kasa shawo kan yadda za a magance hanyar da za a kasafta kudaden da gwamnatin tarayya ke raba wa kan ta da jihohi da kuma kananan hukumomi.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa ba a ma tattauna batun ba a taron da majalisar ta gudanar yau a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.
Da wadannan kudaden ne ake biyan albashin ma’aikata da sauran ayyukan yau da kullum a jihohi da kananan hukumomi har da tarayya baki daya da hakan yasa har yanzu wasu jihohin basu iya biyan albashin ma’aikatan su na watan Yuni ba.
Wannan Majalisa ta kunshi mataimakin shugaban kasa wanda shine shugaban ta da kuma daukacin gwamnonin Najeriya da ministan Abuja.
Saboda karancin kudade a aljihun jihohi tare da kasa samun kudade na watan Yuni da tarayya, akasarin jihohi har yau ba su biya albashin watan Yuni ba.
Bayan fitowa daga taron, Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa batun kasafta kudaden watan Yuni ba ya ma cikin ajandar taron na su na yau.
Sai dai kuma tun a jiya ne gwamnoni suka yi ta ganawa a tsakanin su domin tattauna maganar kasafta kudin na wannan watan.