Mun damu kwarai da yadda aka rika sayen kuri’un zabe a Ekiti – INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana damuwar ta matuka a kan yadda aka rika sayen kuri’un masu zabe a yayin zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda ya gudana ranar Asabar da ta gabata.

Hada hukumar ta bayyana a cikin wata takarda da kakakin hukumar Malam Mohammed Haruna ya sa wa hannu.

Dama kuma wata kungiyar mai zaman kanta mai suna SERAP, ta bukaci INEC da ta yi aiki tare da hukomomin da suka wajaba, domin a tabbatar da an hukunta wadanda aka kama bayan an zakulo.

A cikin jawabin da INEC ta fitar ranar Laraba, ta ce “INEC ta damu sosai da irin yadda aka rika samun yawan harkallar cinikayar kuri’un zabe, kuma ta kudiri aniyar yin aiki kafada-da kafada da hukumomin tsaro domin hana wannan mummunar harkalla.”

Share.

game da Author