An bankado cuwa-cuwar naira biliyan shida a hukumar NISTF

0

Wani Kwamitin Bincike da aka kafa ya bincikin ayyuka da aika-aikar da aka tafka a Hukumar Tara Kudaden Inshora ta Najeriya, NISTF, ta mika wa Ministan Kwadago, Chris Ngige rahoton ta jiya Laraba.

Shugaban Kwamitin Bincike, Ishaya Awotu, ya bayyana cewa sun gano cewa an yi wa ma’aikatan hukumar tare da shugabannin gudanarwar hukumar aringizo na kudi har naira biliyan 5.7.

“An biya su wannan kudaden ne a matsayin alawus ba tare da amincewar Hukumar Daidaita Albashi ta Kasa ba.

Wasu kudaden da aka rika biya ba kan ka’ida ba, sun hada da alawus na sayen katin DSTV da kuma alawus na sayen tufafin zuwa ofis.

Akwai alawus na sayen janareto, na kudin shan mai a cikin mota, wadanda babu su a cikin dokokin aikin gwamnati na cikin hukumar,

Ya ce kwamitin sa ya gano cewa tsakanin 2015 da 2017, ba a tantace ilahirin kudaden da hukumar ta kashe daga cikin wadanda hukumar ta samu ya shigo mata ba, a hedikwatar hukumar a Abuja.

Daga nan sai shugaban ya karanto dokar kasa wadda masu hannu cikin wannan harkalla suka karya.

“Akwai fa lokaci daya da aka kinkimi naira biliyan 15.7 daga cikin asusun wani banki aka maida a cikin wani asusu. Amma kuma aka kasa kawo shaida daga cikin takardu da suka nuna cewa an amince a sauya wa kudaden wurin ajiya.

“Kwamitin binciken ya bankado yadda aka ce an sayi kwamfutoci har na naira bilyan 2.9. Amma kuma a hedikwatar hukumar ba za ka ga alamun samun canjin wasu sabbin kwamtutoci ba.

Ya kara da cewa an sake cirar naira biliyan 2.6, aka biya wasu kudade a wurare daban daban da ba a ga sunayen wuraren ba.

Wannan kwamiti da Minista Ingige ya kafa tun ranar 15 Ga Faburairu, ya rubuta a cikin rahoton sa cewa a hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu cikin tabargazar.

Share.

game da Author