TAMBAYA: Bambamcin akida na Iya sa a kafirta musulmi? Tare da Imam Bello Mai-Iyali
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Mas’alar Kafirta Musulmi, ko Bidi’antar da Musulmi, ko Munafikantar da Musulmi, ko Fasikatar da Musulmi ko Zindikantar da Musulmi, ko Yahudantar da Musulmi da sauransu, maudu’i ne mai mahimmaci.
Malamai sun dade suna bayanin girman hatsarinsa. Kuma wannan babi ne da bai hallata wanda bai da ilimi mai zurfi ba ya yi Magana a cikin sa. Bai halatta a kafirta wani musulmi ba sai wanda Allah da Manzonsa suka kafirta. Ana yin hukunci da kafircin duk wanda ya yi abinda dukkan malamai suka hadu a kan ya warware musuluncin sa.
Wajen kafircin musulmi akidar mutum ba ita bace jagora ba, domin malamai sun yi ittifaki akan abubuwan da ke fitar da mutum daga musulunci.
Duk wanda bincike da hujjoji suka tabbatar da kafircinsa to, ya kafirta ko dan wace akida ne.
Bugu da kari, ana samun masu yin abinda zai kafirta su daga kowace irin akida.
HATSARIN DA KE CIKIN KAFIRTA MUSULMI
Idan wani ya kafirta musulmi batare da hakki ba, to ya fada cikin:
1 – Babban laifin yima Allah karya da kuma magana batare da ilimi ba (mafi girman Zalunci).
2 – Ta’addanci ga musulmi, ta hanyar fitar da shi daga musulunci, raba shi da matar sa, ba zai yi gado ba kuma ba za a gaje shi ba, idan kuma ya mutu, to ba za ayi masa Sallah ba kuma ba za ayi masa wanka ba, da sauran hukunce-hukuncen da za su biyo bayan kafirta shi.
3 – Kalmar kafirci za ta koma kan duk wanda ya kafirta wani batare da hakki ba. Wato zunubin zai koma wajen mai kafirtawa ba wanda aka
kafirta ba.
4 – Fitar da mutum daga musulunci yafi tsananin laifi akan kashe shi.
Malamai sunyi cikkaken bayanin abubuwan da ke warware musulucin mutum da matakan da ake bi wajen tabbatar da Kafirci ko Bidi’anci ko Munafikanci ko Fasikanci ko Zindikanci da sauransu.
Bambancin Akida ba shi ne jagoraba wajen warware Imanin masu imani. A ji tsoron Allah, a kame harshe daga kafirta musulmi matukar sunyi Kalmar shahada kuma suna Sallah. A na bukatar bincike mai zurfi da ilimi mai tarin yawa kafin zartar da hukuncin Kafirci ko Bidi’anci ko Munafinci ko Fasikanci ko Zindikanci ga musulmi.
Allah ka tsare mana imaninmu da mutuncinmu. Amin.
Imam Muhammad Bello Mai-Iyali
Harkatul Falhil Islam
Barnawa Kaduna.