JIKI MAGAYI: Kotun koli ta wanke Saraki daga zargi kin bayyana kadarorin sa ta-ta-tas

0

A hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke a safiyar Juma’ar yau, ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki bai aikata laifi ba game da karar da gwamnatin tarayya ta daukaka cewa yaki bayyana kadarorin sa kamar yadda dokar kasa ta gindaya wa duk wani jami’in gwamnati.

Idan ba a manta ba kotun kula da da’ar ma’aikata CCT ta wanka Saraki daga wannan zargi da ake masa tun a shekarar 2017, inda a bisani gwamnatin tarayya taki amincewa da wannan hukunci ta daukaka kara a kotun koli.

Yanzu dai kotun koli ta yanke hukuncin cewa Saraki bai yi laifi ko na sisi ba.

Share.

game da Author