A yau Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Owerri, ta soke zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar Imo.
Magoya bayan gwamnan jihar Rochas Okorocha ne suka shigar da kara a kotu, a gaban Mai Shari’a Lewis Allago, inda suka yi ikirarin cewa ba a ma gudanar da zaben ba a jihar Imo.
Allago ya shafe awa biyu biyu ya na karanto ba’asin korafin da masu shigar da kara suka yi, tare da karanto hujjojin da wadanda aka maka kotu suka gabatar.
A karshe dai ya soke zaben, tare da umartar cewa gaba daya a sake zaben shugabannin mazabu na jihar Imo.
“Su je su sake gudanar da sabon zabe a bisa ka’idar da dokar da jam’iyyar ta shimfida, kuma su kasance mutane nagari da za su kare wa dimokradiyya mutuncin ta.” Inji Mai Shari’a.
Mai Shari’a ya ce ya yanke hukunci ne ta hanyar yin amfani da rahoton da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta gabatar cewa ba a gudanar da zaben ba.
Mai Shari’a ya kara da cewa lauya mai kare wadanda ake kara ya kasa kawo hujja kwarara da ke nuna cewa an gudanar da zaben.
Idan za a iya tunawa, magoya bayan jam’iyyar APC da dama sun yi wa zaben na shugabannin mazabu da jihohi da kananan hukumomin jam’iyyar APC tofin Allah-tsine a bisa dalilin cewa kusan a dukkan jihohin kasar nan magudi, son kai da dauki-dora kawai aka yi.
Wasu da dama sun bayyana cewa ko a lokacin PDP ba a yi rashin adalcin da aka tafka a zaben shugabannin jam’iyyar APC na mazabu da kananana hukumomi ba.
Kada kuma a manta da yadda zaben ya kawo rikici sosai a jihohi da da dama, har da kisa, raunata manya a kananan ‘yan jam’iyyar APC da kuma kone-kone.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana cewa an yi rashin adalci, amma maimakon ya ce a gyara, sai ya ce za a tari gaba, wadanda aka yi wa rashin adalci su yi hakuri.
A yanzu dai kotu ta fara soke zabukan daga jihar Imo.