Sake takarar Buhari zai fi rudanin 12 Ga Yuni muni – Ogbonnia

0

Tsohon masoyin Shugaba Muhammadu Buhari mai suna SKC Ogbannia, ya furta cewa ba karamin ganganci ba ne a sake bai wa Buhari takara a zaben 2019.

Ogbonnia wanda a yanzu haka ya na cikin ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, ya ce idan aka kuskura aka ba Buhari takara, to za a yi da-na-sani, domin sakamakon da zai biyo baya sai ya fi zaben 12 Ga Yuni mini.

A wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES, ya ke maganar gaskiya Buhari ya sani cewa ba shi da kuzari da fikirar ta fi da mulkin jama’ar karni name 21.

Ya ci gaba da cewa Buhari ya zubar da damar sa, domin an yi masa tunanin cewa zai iya fitar da kasar nan daga matsalolin da gwamnatin baya ta haddasa.

“Buhari ya fara tuki da baya-baya, tun bayan da aka zabe shi, yayin da ya yi watsi da makusantan sa kuma masana na gaskiya, sai ya jawo ‘yan damaga, wadanda kwakwalwar su ta fi karkata tun irin ta mutanen da aka yi a karkonin jahiliyyar farko-farko.”

“Sai ya kasance shugaba maras bin abin da doka ta ce.Ya dora ‘yan bulkara a mukamai su na shirme. Ga shi ya na mulkin Fir’aunaci, amma kuma ga shi talasurun shugaba wanda ba sai da karfi.

“Alamu fa na nuna Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai iya tsige Buhari kan mulki. Ni na fada muku wannan, sai fa idan bai ga dama ya lashes dare ya na kulla tuggu da kutunguila ba.

“Kuma bari ku ji wani abu, ba wanda ya haifar wa APC matsala sai Buhari. Idan ya hangi baraka shi fa babu ruwan sa da dinke ta. Su kuma manyan cikin jam’iyyar sun hango cewa Buhari bai iya komai, sai su ke yin yadda suka ga dama. Domin ba so su ke yi ya sake tsayawa takara ba.

“Hatta wadanda suka fi shisshige masa din nan, su Nasir El-Rufai, Rochas Okorocha, Tinubu, duk ta ciki na ciki kawai, amma ba su so ya sake tsayawa takara. Shi ya sa ni ma na fito takara a APC, domin mu taka masa burki.”

Ogbonnia ya yarda cewa Buhari ya yi kokari a shekaru uku da ya yi, amma a yanzu dai ba shi da kamannu na jagoran da zai iya fitar da Najeriya daga cikin matsalolin da ta a yanzu.

“Na tabbata mu na da masu irin halin sa da yawa. Don haka kamata ya yi ya hakura, domin ko Barack Obama zai zo ya rika tallata Buhari, to ba sai sake yin irin farin jinin sa na baya ba.”

Share.

game da Author