Matashi ya kashe mahaifin sa da kanwar sa da adda

0

Mutanen kauyen Ifelemenu da ke cikin Karamar Hukumar Ekpaomaka a jihar Ebonyi sun ga tashin hankaki, yayin da wani matashi mai shekara 25 da haihuwa ya yi kaftar uban sa da kanwar sa da adda har ya kashe su.

Wannan mummunan kisa ya faru ne kamar yadda wanda abin ya faru a kan sa ya bayyana, ya ce makashin mahaifin na sa mai suna Julius, ya tubure bayan da ya koma gida a makare, har mahaifin na sa ya fara yi masa fadan neman sanin inda ya je yawo.

Yayin da hatsaniya ta kaure tsakanin Julius da mahaifin sa, sai bakar zuciya ta kwashe shi, ya zabura ya dauko adda ya yi ta saran uban na sa, har ya mutu.

Kanwar Julius mai shekaru bakwai a duniya ta gigita ta zaburo ta na neman dalilin da ya sa ya kashe musu uba. Ita ya fizge ta, ya yi ta sara har ta mutu.

Makwabta sun tabbatar da cewa ya kuma ji wa mutane shida mummunan rauni yayin da suka yi kokarin kai dauki.

Amma kuma an ruwaito cewa wani makwabcin su ya yi gaggawar dauko bindiga, ya harbe shi, saboda haushin saran matar sa da ya yi da adda.

Duk da dai ba a san takamaimen yin kisan ba, amma an tabbatar da cewa a lokacin da ya yi kisan ya na cikin mayen wasu muggan kwayoyin da ya sha.

An ajiye gawarwakin mamatan a Asibitin Koyarwa na Abakaliki, yayin da su kuma wadanda aka ji wa ciwo ke samun kulawar likitoci a wani asibin da ba a bayyana ko a ina ya ke ba.

Kakakin ‘Yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar wannan mumunan kisa.

Sai dai kuma ta ce Julius ya kashe kan sa ne bayan ya kashe uba da kanwar sa, kamar yadda ta ce rahoto ya je musu.

Ta ce ana nan ana tsananta bincike tukunna.

Share.

game da Author