‘Yan majalisar dokokin jihar Kano sun tsige kakakin majalisar Abdullahi Ata sannan suka nada tsohon kakakin majalisar Kabiru Rurum.
Bayan Ata da aka tsige, an musanya shugabannin majalisar biyu sannan an nada sabon mataimakin kakakin majalisa.
An dade ana kai ruwa rana a majalisar dokokin jihar Kano tsakanin mambobin majalisar da kakakin majalisar, da ake ganin da dadewa an so ay tsige shi amma bai yiwu ba.