Yau ne da misalin karfe 11 na safe aka fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana.
An fara ne mako guda cur da fara aikin Hajji din a Saudi Arabiya.
Kakakin Hukumar Alhazai ta Kasa, Fatima Sanda, ta ce yau Asabar ne jirgin Max Air zai fara daukar maniyyata daga jihar Kogi.
Za a kaddamar da jigilar da misalin karfe 11: na safe a filin jirginNnamdi Azikwe dake Abuja.
Ta ce wadanda aka kwasa din za a zarce da su ne kai tsaye zuwa Madina.

Da ta ke magana a kan aikin tantance maniyyata, Usara ta ce ya zuwa yanzu dai an tantance 17,000 yayin da 5,000 har sun karbi bizar su.
Ta yi kiran a kara hakuri kuma a ci gaba da bi a hankali wajen aikin tantancewar.