Ma’aikatar gyara birane ta jihar Adamawa ta umarci ofishin kamfen din gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo da ya fito takarar shugabancin kasa Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP da ya gaggauta cire fostar sa da ya kafa a tsakiyar garin Yola.
Gwamnati tace wannan wuri da aka kafa wannan fosta wuri ne da aka kebe wa masu tuka keke Napep a jihar ba wajen kafa fosta ba ne.
A dalilin haka suna umartar sa da ya gaggauta tumbuke wannan fosta ko kuma a tumbuketa da karfin tsiya.
Sai dai bayan samun wannan takarda, shugaban kamfen din Ibrahim Dankwambo a jihar na Adamawa Dahiru Kere ya ce bai dace ba ace wai gwamnati ta aika musu irin wannan barazanar.
” Najeriya kasa ce ta kowa da kowa, sannan mu ‘yan kasa ne cikakku, babu dalilin da zai sa a hana mu kafa fostan mu a duk inda muke so a fadin kasar nan.
” Da farko sun bukaci mu biya naira miliya 1 ne na kafa wannan fosta, amma bayan mun amince za mu biya sai kuma daga baya suka ce ba haka ba wai kawai mu cire fostar shine bukatar su.
Discussion about this post