Bukola Saraki na da hannu a kafa R-APC – Inji Sanata Adamu

0

Sanata Abdullahi Adamu da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma, ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki na da hannu wajen ya kafa R-APC, jam’iyyar da hasalallun ‘yan APC suka kafa kwanan baya.

Ya Saraki ne ya kafa jam’iyyar ta bayan fage, amma a halin yanzu ya na jin tsoron fitowa fili ne don kada ya rasa kujerar sa ta Shugaban Majalisar Dattawa.

Adamu ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a babbar sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya kara cewa Saraki da duk sauran wanda ke sha’awa za su iya barin APC.

“Duk fa abin da mutanen nan ke fada a kai, ba wani abin kishin kasa ko al’ummar kasa ba ne, duk su na yi ne don kishin kan su kawai. Kuma ina tabbatar muku sun tsaya cikin APC ne kawai don su yi mata mummunar illa kawai.”

Lokacin da nPDP suka fara korafe-korafe, Adamu ya fito ya ce dama a rabu da su kawai, domin su na so ne su yi wa APC zagon kasa, saboda ai sun amfana, tunda an ba su mukamin shugaban majalisar dattawa, wanda Saraki din ne ya samu mukamin shugaban na Majalisar Dattawa.

Don haka sai Adamu ya ce to ga shi nan abin da ya fassara su a baya, ta tabbata a yanzu.

Sai dai kuma ya ce ko a yanzu din ma a daina kula su, duk wanda ke son ficewa daga APC, to ga fili nan kuma ga mai doki.

” Tun lokacin da aka rantsar da wannan gwamnati ta APC ne aka fara samun baraka bayan daya daga cikin masu son zama shugaban majalisa ya hada baki da jam’iyyar adawa ya zama shugaban jam’iyyar. Daga nan ne fa majalisar tarayya ta zama bangaren adawar gwamnati.

Da ya koma kan sabon shugaban jam’iyyar na kasa baki daya, Adams Oshiomhole kuwa, ya ce za su hada kai su ba shi cikakken goyon baya.

Share.

game da Author