ZAMFARA TA DAU ZAFI: An sace wani dan Chana a yankin Bakura

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar wa sace Ren Dajun, wani dan kasar Chana da ake aiki a wani kamfanin gini a jihar Zamfara.

Kakarin rundunar ‘yan sandan, Mohammed Shehu, ya shaida cewa Dajun na aiki da wani kamfanin gini ne a kauyen Birnin Tudu, cikin Karamar Hukumar Bakura.

Ya ce an sace shi a jiya Laraba da misalin karfe 2 na rana a cikin wani dajin noman rani kusa da kauyen Amumu da ke cikin yankin Bakura.

“Amma mun dukufa ta hanyar tura ‘yan sandan hana yin garkuwa mun kuk-kutsa cikin daji domin kokarin tabbatar da mun kwato shi cikin koshin lafiya, kuma mun kamo wadanda suka yi garkuwar da shi.”

Ya roki mutanen yankin da su rika yin kaffa-kaffa da bakon-ido ko wani da ba su yarda da shi ba, ta hanyar gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro.

Share.

game da Author