Hunkuyi, Ashiru, Shehu Sani ba za su iya ja da El-Rufai a 2019 ba – Aruwan

0

Kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ya gargadi ‘yan siyasan Kaduna musamman wadanda ke neman fitowa takarar gwamnan jihar Kaduna da su shiga taitayin su sannan su sani cewa idan dai kujerar gwamna ne toh bindin rakuma yayi nesa da kasa.

Aruwan ya bayyana haka ne a tattaunawa da yayi da ‘yan jarida a garin Kaduna.

Bayan haka ya kara da cewa idan har gidan gwamnati ne suke kwadayin shiga lallai akwai sauransu tukuna domin El-Rufai ya riga yayi gaba.

” Masu son su dare kujerar gwamna a jihar Kaduna na son haka ne kawai don son mulki amma ba wai don su yi wa jama’a aiki ba. Fanko suke fawai, babu wani abu a zukatan su, suna so ne su shigo gidan gwamnati don su azurta kan su ba wai don wani abu fiye da haka ba.

Wadanda kakaki Aruwan ke zance a kai kuwa duk da cewa basu fito karara sun nuna maitan su a fili ba tukunna ba kamar yadda ya zayyano su sun hada da Sanata Sule Hunkuyi, Sanata Shehu Sani, Ramalan Yero, Sani Sidi, Isah Ashiru da dai sauran su.

” Tun da suka ga ba za su yi kama kafar El-Rufai wajen kwararo wa mutanen jihar Kaduna romo da lagwadar dimokradiyya ba sai suka koma suna yi masa bita-da-kulli, nukufarci, makininita, zamba da hassada duk don wai don su kau dashi daga gaban su wato su su dare kujerar mulki.

Aruwan ya kara da cewa gwamna El-Rufai yayi abin azo a gani a jihar Kaduna da baya misaltuwa. El-Rufai ya tallafawa mata, yara, marasa galihu, ya samar wa matasa da aikin yi ya gyara fannin ilimi a jihar sannan sauran su.

Share.

game da Author