Shimfida adalci a cikin jam’iyya kadai zai iya cetar APC – Dogara

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya gargadi jam’iyyar APC da cewa duk wani kame-kame da borin-kunya ba zai magance gagarimar matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar ba, har sai an jaddada adalci tsakanin ‘ya’yan jamiyya tukunna.

Kakakin yada labaran sa Hassan Turaki ya aika wa kafafen yada labarai da wasika mai dauke da cewa Dogara ya yi wannan bayani ne a wurin taron mambobin tarayya na jam’iyyar APC da kuma shugabannin jam’iyyar a karkashin shugaban ta Adams Oshiomhole.

Ya ce an gudanar da taron ne a babban dakin taro na Majalisar Tarayya.

“Babu wani abu da mambobin Majalisar Tarayya karkashin APC ke bukata daga shugabannin jam’iyya sai aiwatar da adalci kawai.

Dogara ya ci gaba da cewa, “matsawar babu gaskiya da adalci, to APC za ta kara dannawa cikin rudu ne kawai, kuma babu wani katabus ko hobbasa da za mu iya hana masu ballewa ficewa.”

Oshiomhole ya sha alwashin duba matsalolin jam’iyyar ya na mai cewa duk wani dan jam’iyya, na sa ne ba shi da ‘ya’yan mowa ko na bora.

Share.

game da Author