Kotu ta daure Uwa da ‘Ya da suka kashe mahaifinta

0

Kotu dake babban birnin tarayya Abuja ta daure wata mata da ‘yar ta da ta kama su da laifi hada baki su kashe mahaifin ta dake zaune a kauyen Bwari.

Alkali Idris Kuta ya bayyana cewa ana zargin matan biyu ne da kasahe mahaifin yarinyar saboda wai yaki amincewa ‘yar sa ta auri wani saurayin ta da take so.

Dan sandan da ya shigar da kara ya ce sun kashe mahaifin yarinyar ne ranar 10 ga watan Maris a gidan su dake Karavan, Bwari Abuja.

Dukkan su biyun sun musanta haka, sai dai Alkali Kuta ya ce ci gaba da tsare su har sai kotu ta yanke hukuncin shari’ar.

Share.

game da Author