Shugaban ma’aikatan ofishin shugaban majalisar dattawa, Hakeem Baba Ahmed ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC a yau litinin.
Hakeem ya ce tuni har ya aika da sakon ficewar sa daga jam’iyyar APC din ga bangaren jam’iyyar APC a Kaduna wato APC Akida.
Bayan haka ya ce wannan ficewa daga APC da yayi ba shi da nasaba da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki da yake wa aiki.
” Wasu daga cikin dalilan da ya sa na fice daga APC shine ganin jam’iyyar ta gagara cika alkawurran da ta dauka wa mutanen kasar nan. Ya ce gwamnati ta gaza matuka sannan shi ba zai iya ci gaba da zama cikin irin wannan jam’iyya ba.
” Wannan shawara da na dauka ya zama dole a gareni duk da cewa APC jam’iyya ce da aka kafa tare da ni, amma dole in hakura da ita domin kuwa ba abin da muka yi wa jama’ Alkawari zamu yi musu gwamnantin da muka kafa ke yi ba.
” Sannan kuma ina nan a dan siyasa na, kuma cikakke domin yanzu ta siuasar ce kawai irin mu za su iya gyara kasar mu.

Sanata Shehu Sani wanda shima dan Kungiyar APC Akida ne ya yi barazanar ficewa daga APC a kwanakin baya. Amma kuma tuni Hon Isah Ashiru wanda shima dan kungiyar ne ya fice daga jam’iyyar inda ya koma jam’iyyar PDP.
Yanzu haka kusan hotunan sa ya karade jihar na takarar gwamna.
Discussion about this post