Kotu ta kara bada belin Sambo Dasuki

0

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ta sake bada belin tsohon Mai Bada Shawara a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki, tare da neman a ajiye naira miliyan 100 a kotu.

An dai kama Dasuki ne tun cikin Disamba, 2015, yayin da jami’an SSS suka yi awon gaba da shi, kuma tun a lokacin ya ke a tsare, duk kuwa da kotu ta sha bada umarnin a sake shi.

Ana zargin sa da zama babban gogarman karkatar da dala bilyan 2.1

Dasuki ya sha neman hakkin sa a wurare daban-daban, har da kotun ECOWAS ta Afrika ta Yamma, wadda tun a cikin 2017 ita ma ta yanke hukuncin cewa a bayar da belin sa, amma gwamnatin tarayya ta ki.

A yau kuma kotu a karkashin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta saurari batun da lauyoyin Dasuki suka shigar cewa, wannan kotu ta bayyana wa duniya shin ci gaba da tsare Dasuki ba tare da yanke masa hukunci ba, daidai ne ko rashin adalci ne?

Bayan Ijeoma ta yi nazari, ta bayyana cewa a gaggauta sakin Dasuki, amma a samu masu tsaya masa beli mutum biyu, kuma sai an ajiye naira miliyan 100 a kotu tukunna kafin a sallame shi.

Ta ce masu belin za su iya kasancewa ma’aikatan gwamnati da suka kai mataki na 16, ko kuma masu harkokin kan su, amma su kasance sun mallaki wata kadara ta gida ko fili a Abuja.

Ta kuma ce a bar fasfo na Dasuki a kotun ta, don kada ya nemi ficewa kasar a lokacin da ya ke a karkashin zaman beli a gida.

Share.

game da Author