Saraki ya nemi a tsige hafsoshin tsaron kasa

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari, da ya gaggauta tsige shugabannin hukumomin tsaron kasar nan, domin ya maye gurbin su da wadanda za su iya magance munanan kashe-kashen da ake yi a kasar nan.

Da ya ke magana a wata ziyarar jaje da ya je a yankin da ruwa da guguwa suka yi wa barna a Ilorin, a jiya Asabar, Saraki ya yi gargadin da a guji maida siyasantar da wasu batutuwa a kasar nan.

“Wannan ba fa batu ba ne na siyasa, idan aka ba mutum mukami kuma ya nuna bai iya yin abin da aka dora shi don ya yi, to a cire shi domin a bai wa wasu da za su iya.”

Saraki ya zargi dukkan shugabannin hukumomin tsaron kasar nan da kasa magance mummunan kashe-kashe da ake yi a kasar nan.

“Mu ajiye batun siyasa daban, yanzu muna magana ne a kan yawaitar kisan jama’a bagatatan a kasar nan. Kowa ya san shugabannin hukumomin tsaro sun gaza, don haka cire su a maye gurbin su da wadanda za su share wa al’ummar kasar nan kukan karkashe jama’a da ke gudana.”

Share.

game da Author