A jiya Asabar ne wuta ta kone shaguna 14 sakamakon wata tukunyar gas da ta fashe a Kaduna.
Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, ya ruwaito cewa tukunyar ta fashe a kan titin Ibrahim Taiwo, daidai mahadar titin Abeokuta, a Kaduna.
Hadarin ya auku da misalin karfe 5:30 na yamma.
Rahoton NAN ya ce makwauta ne suka yi dandazon kai daukin kashe gobarar.
Kantunan da gobarar ta shafa akasari na masu sayar da kayan dafe-dafe ne, sai na masu saida tukunyar gas da kuma dura iskar gas.
Sai dai kuma hasalallun mutane sun kori jami’an kashe gobara, da suka kai dauki daga Jami’ar Kaduna, a bisa dalilin sun isa wurin a makare, kimanin awa daya bayan kashe gobarar.
Discussion about this post