Sarkin Dukku a Jihar Gombe, Haruna Abdulkadir, ya yi barazanar tube rawanin duk wani dagaci ko hakimin da ke kin fallasa dillalan kwaya a yankin sa.
Sarkin ya yi wannan kakkausan gargadi ne a garin Dukku, a lokacin da ya ke jawabi wurin taron zagayowar ranar wayar da kai kan muggan kwayoyi ta duniya, ta 2018.
“Babban aikin ku shi ne ku rika tona asirin masu jibge muggan kwayoyi su na sayarwa ga ‘ya’yan mu, ba wai ku rika boye su daga damkewar hukuma ba. Domin idan ku ka yin haka, to ku na taimaka musu ne ana gurbata al’umma.”
Ya ce masarautar sa na hada kai da Hukumar NDLEA kuma za su fara amfani da babura domin kutsawa cikin lungunan Dukku da kauyukan ta a damko masu dillancin kwayoyi.
Sarki Haruna ya ci gaba da cewa mutane na amfani da maganin Tramol a matsayin maganin karfin maza, ba su ran cewa kan su suke yi wa illa ba.
Ya ce akwai wadanda shan kwayoyi ya zame musu jiki, har ta ci su ta cinye, ta yadda ba za a iya farfado musu da cikakkiyar lafiyar su ba.
Daga nan sai ya bada tabbatacin cewa da taimakon hukumar NDLEA, za a yi kokarin a magance wadannan ‘yan kwaya a warkar da su.
Ya jinjina wa NDLEA da suke gayyato dalibai a lokacin taruka, wadanda hukumar ta nuna cewa dama don su ake gudanar da taron wayar da kan, saboda su ne yara kuma masu tasowa.
Discussion about this post